RFI Hausa
banner
ha.rfi.fr
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
🌍 Sashen Hausa na RFI na maraba da ku a shafin Bluesky
💻 rfi.fr/ha/ 🎧 rfi.my/kai-tsaye
𝕏 rfi.my/Xha 📷 rfi.my/IGha 🗨️ rfi.my/WAha
Isra'ila ta ƙaddamar da mummunan farmaki a kudancin Lebanon
Isra'ila ta ƙaddamar da mummunan farmaki a kudancin Lebanon
Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a garuruwa biyu na kudancin Lebanon, inda ta lalata gine-gine tare da kashe aƙalla mutane 13, abinda ya tilastawa mutane da dama ficewa daga muhallansu.
www.rfi.fr
November 19, 2025 at 5:50 PM
Ana ci gaba da ganin tsadar biredi duk da saukar farashin kayayyaki a Najeriya
Ana ci gaba da ganin tsadar biredi duk da saukar farashin kayayyaki a Najeriya
Al'umma a jihar Kano dake Najeriya na ci gaba da kokawa kan rashin saukar farashin biredi da gurasa, duk da saukar farashin fulawa da sauran kayan da ake sarrafawa. 
www.rfi.fr
November 19, 2025 at 4:29 PM
Guterres ya yi kira ga ƙasashen Sahel su haɗa kai don tunkarar matsalar tsaro
Guterres ya yi kira ga ƙasashen Sahel su haɗa kai don tunkarar matsalar tsaro
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga ƙasashen Sahel da su ajiye bambance-bambancensu a gefe guda domin tinkarar hare-haren da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ke kaiwa a yankin na Afirka da ke fama da matsanancin halin jinƙai.
www.rfi.fr
November 19, 2025 at 3:22 PM
Sabon harin Rasha a Ukraine ya yi sanadin rayukan aƙalla mutane 19
Sabon harin Rasha a Ukraine ya yi sanadin rayukan aƙalla mutane 19
Aƙalla mutane 19 suka rasa rayukansu a yayin wani mummunan farmaki da Rasha ta kai kan wani dogon gini ta hanyar amfani da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuƙa a birnin Ternopil da ke yammacin ƙasar Ukraine.
www.rfi.fr
November 19, 2025 at 3:08 PM
Tinubu ya soke tafiya taron G20 saboda sace ɗaliban Kebbi da kuma harin cocin Kwara
Tinubu ya soke tafiya taron G20 saboda sace ɗaliban Kebbi da kuma harin cocin Kwara
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya dakatar da tafiya taron G20 a Afrika ta Kudu, sakamakon harin da aka kai wata mujami'a a jihar Kwara, da kuma sace 'yanmatan makarantar sakandiren Kebbi da aka yi, a wani yanayi da matsalar tsaro ke ƙara ta'azzara a sassan ƙasar.
www.rfi.fr
November 19, 2025 at 1:07 PM
Rikicin zaɓen Tanzania ya ɓata mana suna a idon duniya- Suluhu
Rikicin zaɓen Tanzania ya ɓata mana suna a idon duniya- Suluhu
Shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan ta ce rikicin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa na watan Oktoba, ya ɓata wa ƙasar suna a idon duniya, kuma zai iya hana ta samun tallafi daga ƙungiyoyi da ƙasashen waje.
www.rfi.fr
November 19, 2025 at 11:46 AM
Sojojin Mali na haɗa kai da ƴan sa kai wajen kisan fararen hula-HRW
Sojojin Mali na haɗa kai da ƴan sa kai wajen kisan fararen hula-HRW
Ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, ta zargi sojojin Mali da kuma ƴan sa kai da ke taimaka musu wajen kashe wasu fararen hula 31 tare da ƙona gidaje a wasu ƙauyuka biyu da ke yankin Segou na tsakiyar ƙasar.
www.rfi.fr
November 19, 2025 at 7:16 AM
Har yanzu babu alƙalman mutanen da suka mutu a zanga-zangar Tanzania-Ƙungiyoyi
Har yanzu babu alƙalman mutanen da suka mutu a zanga-zangar Tanzania-Ƙungiyoyi
Ƙungiyaoyin farar hula da na kare haƙƙin bil’adama a Kenya sun soki jan ƙafa da hukumomin Tanzania ke yi wajen tattabar da mutanen da aka kashe sakamakon tashin hankalin  da ya ɓarke a yayin babban zaɓen ranar 29 ga watan Oktoba.
www.rfi.fr
November 19, 2025 at 7:02 AM
Sabon rikici a babbar jam'iyyar adawar Najeriya PDP ya sake ɓallewa
Sabon rikici a babbar jam'iyyar adawar Najeriya PDP ya sake ɓallewa
Sabon shugaban jam’iyyar adawa mafi girma a Najeriya PDP Kabiru Tanimu Turaki, yayi kira ga shugaban Amurka Donald Trump da ya kawowa ƙasar don ceto demokuradiya.
www.rfi.fr
November 19, 2025 at 6:49 AM
A karon farko an tabbatar da kasancewar sojojin Rasha a ƙasashen Afrika 6
A karon farko an tabbatar da kasancewar sojojin Rasha a ƙasashen Afrika 6
A wani yanayi na bazata, babbar kafar talabijin mallakin Rasha, ta tabbatar da kasancewar dakarun Moscow a ƙasashen Afrika har guda 6, waɗanda ke taimakawa a ɓangarori da dama na ƙasashen, musamman a ɓangaren tabbatar da tsaro.
www.rfi.fr
November 19, 2025 at 6:36 AM
Yariman Saudiya ya isa Amurka karon farko bayan zarginsa da kisan Kashoggi
Yariman Saudiya ya isa Amurka karon farko bayan zarginsa da kisan Kashoggi
Yarima mai jiran gado na Saudiya Muhammad Bin Salman ya isa birnin Washington na Amurka don ganawa da shugaba Donald Trump, a wani yanayi da ake saran ƙulla sabbin yarjeniyoyin kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
www.rfi.fr
November 18, 2025 at 5:05 PM
An jibge gawarwakin mutane fiye da 100 a asibitin Yaounde na Kamaru
An jibge gawarwakin mutane fiye da 100 a asibitin Yaounde na Kamaru
Rahotanni daga birnin Yaounde na Jamhuriyar Kamaru na cewa, an jibge gawawwakin mutane sama da 100 a wani babban asibitin yankin, lamarin da ya ɗiga ayar tambaya kan ko ‘yan ‘uwan mamatan na da masaniya game da inda suke.
www.rfi.fr
November 18, 2025 at 3:58 PM
Martanin Hamas da wasu ƙasashe kan amincewa da daftarin Gaza da MDD ta yi
Martanin Hamas da wasu ƙasashe kan amincewa da daftarin Gaza da MDD ta yi
Hamas ta ce shirin zaman lafiyar Gaza da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar wanda Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da shi a yau, ya gaza kare dukkan muradun Falasɗinawa, walau ta fuskar siyasa ko ayyukan jinƙai.
www.rfi.fr
November 18, 2025 at 3:04 PM
Muna kira ga Trump da ya ceto dimokuraɗiyyar Najeriya - Turaki
Muna kira ga Trump da ya ceto dimokuraɗiyyar Najeriya - Turaki
Sabon shugaban Jam’iyyar PDP a Najeriya, Tanimu Turaki ya yi kira ga shugaban Amurka Donald Trump da ya kawo musu ɗauki wajen ceto dimokuraɗiyyar ƙasar wanda ya ce ta kama hanyar durƙushewa.
www.rfi.fr
November 18, 2025 at 12:36 PM
Kylian Mbappe ya shigar da PSG ƙara gaban kotu
Kylian Mbappe ya shigar da PSG ƙara gaban kotu
Taƙaddamar da ke tsakanin ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe da tsohon kulob ɗinsa Paris Saint-Germain (PSG) ta kai ga kotun ƙwadago ta Faransa.
www.rfi.fr
November 18, 2025 at 8:06 AM
Rikici ya sake ɓarkewa tsakanin dakarun gwamnati da M23 a DR Congo
Rikici ya sake ɓarkewa tsakanin dakarun gwamnati da M23 a DR Congo
An ci gaba da gwabza faɗa a gabashin Jamhuriyyar Demokraɗiyya Congo duk da rattaɓa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin wakilcin gwamnatin ƙasar dana ƙungiyoyin M23 da AFC yayin bikin da ya gudana a ranar 15 ga watan nan a Doha.
www.rfi.fr
November 18, 2025 at 8:06 AM