RFI Hausa
banner
ha.rfi.fr
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
🌍 Sashen Hausa na RFI na maraba da ku a shafin Bluesky
💻 rfi.fr/ha/ 🎧 rfi.my/kai-tsaye
𝕏 rfi.my/Xha 📷 rfi.my/IGha 🗨️ rfi.my/WAha
Amurka ta jaddar da bukatar bai wa kiristoci kariya a Najeriya
Amurka ta jaddar da bukatar bai wa kiristoci kariya a Najeriya
Amurka ta jaddada buƙatar ganin gwamnatin Najeriya ta bai wa Kiristocin ƙasar cikakkiyar kariya sakamakon hare-haren da mabiya wannan addinin ke fuskanta.
www.rfi.fr
January 22, 2026 at 4:07 PM
Sojoji da ke mulki a Bissau sun sanya 6 ga watan Disamba ranar shirya zaɓe
Sojoji da ke mulki a Bissau sun sanya 6 ga watan Disamba ranar shirya zaɓe
Sojoji da suka ƙwace mulki a Guinea-Bissau sun tsaida ranar 6 ga watan Disamba mai zuwa a matsayin ranar babban zaɓen ƙasar, lokacin da za’a cika shekara ɗaya da hambarar da shugaba Umaro Sissoco Embalo a ƙarshen shekarar da ta gabata.
www.rfi.fr
January 22, 2026 at 1:11 PM
Gwamnan Kaduna ya ziyarci Kurmin Wali don yin jaje ga mutanen yankin
Gwamnan Kaduna ya ziyarci Kurmin Wali don yin jaje ga mutanen yankin
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, za ta tabbatar da dawo da duk waɗanda aka sace a ƙauyen Kurmin Wali lafiya.
www.rfi.fr
January 22, 2026 at 9:08 AM
Rundunar ƴansandan Turai ta bankaɗo babbar cibiyar sarrafa ƙwayoyi a duniya
Rundunar ƴansandan Turai ta bankaɗo babbar cibiyar sarrafa ƙwayoyi a duniya
Rundunar tsaron yan sandan Turai ta ce tayi nasarar gano wata babbar kungiya dake safarar miyagun kwayoyi tsakanin kasashe, wannan gagarumar nasara a cewar su ita ce mafi girma da ba’a taba yin irin ta ba  .
www.rfi.fr
January 22, 2026 at 8:41 AM
Yau dakatar da bada biza ga ƴan Najeriya da wasu ƙasashe 74 ke fara aiki
Yau dakatar da bada biza ga ƴan Najeriya da wasu ƙasashe 74 ke fara aiki
Yau sabbin dokokin shige da fice na Amurka, wanda Shugaba Donald Trump ya gabatar, na dakatar da aikace-aikacen bada bizar Amurka ga ƙasashe 75, ciki har da na Afirka 26, da suka haɗa da Ivory Coast da Kamaru da Senegal da kuma Najeriya za su fara aiki.
www.rfi.fr
January 21, 2026 at 2:41 PM
Congo ta damƙawa Amurka jerin ma'adinan da ta ke da su don zuba jari wajen haƙarsu
Congo ta damƙawa Amurka jerin ma'adinan da ta ke da su don zuba jari wajen haƙarsu
Wasu manyan jami’an kasar Congo sun bayyana cewar Kasar ta mika wa kasar Amurka jerin sunayen ma’adanan karkashin kasa da Allah ya huwace wa kasar da su ka hada da Kanwa da Karfen Gachi da Zinari da Tasa domin janyo hankalin masu saka hannayen jari na kasar Amurka.
www.rfi.fr
January 21, 2026 at 9:47 AM
Zelensky ya koka da yadda hankalin Turai ya karkata ga Greenland maimakon Ukraine
Zelensky ya koka da yadda hankalin Turai ya karkata ga Greenland maimakon Ukraine
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ta bayyana damuwa da abin da ya kira yadda batun kwatar yankin Greenland da Amurka ke yi ke Shirin karkatar da hankullan Amurka da kasashen Duniya a kan kashin mummuke da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ke yi wa kasarsa.
www.rfi.fr
January 21, 2026 at 9:33 AM
Sojin Habasha sun kashe mayaƙan ƴan tawaye 40 a yankin Amhara
Sojin Habasha sun kashe mayaƙan ƴan tawaye 40 a yankin Amhara
Dakarun Sojin kasar Ethiopia sun tabbatar da kisan wasu ‘yan ta’adda masu ta da kayar baya su 40 ta hanyar amfani da Kurman jirgin yakinsu a yankin Amhara.
www.rfi.fr
January 21, 2026 at 9:33 AM
Macron ya caccaki Trump kan yiwa Turai barazana game da yankin Greenland
Macron ya caccaki Trump kan yiwa Turai barazana game da yankin Greenland
Shugaban Emmanuel Macron na Faransa, ya soki lamarin shugaban Amurka Donald Trump a ƙoƙarinsa na neman yin ƙarfa-ƙarfa a kan ƙasashen Turai.
www.rfi.fr
January 21, 2026 at 8:53 AM
Nijar ta kafa kwamitin tunƙarar rikicinta da kamfanin Orano na Faransa
Nijar ta kafa kwamitin tunƙarar rikicinta da kamfanin Orano na Faransa
Gwamnatin Nijar ta kafa wani kwamiti da zai tattara hujjoji da kuma shawarwarin da ƙasar za ta yi amfani da su a takun-sakar da ke tsakaninta da kamfanin haƙo Uranium na ƙasar Faransa.
www.rfi.fr
January 21, 2026 at 8:39 AM
Mbappe ya ratata ƙwallo a ragar tsohuwar ƙungiyarsa a gasar zakarun Turai
Mbappe ya ratata ƙwallo a ragar tsohuwar ƙungiyarsa a gasar zakarun Turai
Ɗan wasan gaba na Real Madrid Kylian Mbappe ya zura ƙwallaye har 2 a ragar tsohuwar ƙungiyarsa Monaco yayin karawarsu ta daren jiya da suka samu gagarumar nasara da ƙwallaye 6 da 1 ƙarƙashin gasar cin kofin zakarun Turai.
www.rfi.fr
January 21, 2026 at 8:26 AM
Jesus ya zura ƙwallaye 2 a nasarar da Arsenal ta yi kan Inter Milan
Jesus ya zura ƙwallaye 2 a nasarar da Arsenal ta yi kan Inter Milan
Karon farko cikin lokaci mai tsayi, Arsenal ta yi tattaki zuwa Italiya tare da samun nasara bayan da ta lallasa Inter Milan da ƙwallaye 3 da 1 a haɗuwarsu ta jiya a filin wasa na San Siro ƙarƙashin gasar cin kofin zakarun Turai.
www.rfi.fr
January 21, 2026 at 8:12 AM
Syria ta ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 4 da mayaƙan Kurdawa
Syria ta ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 4 da mayaƙan Kurdawa
Kasar Syria ta shelanta cimma yarjejeniyar tsagaita Wuta na kwanaki 4 a fadan da ake gwabzawa tsakanin Sojin kasar da ‘yan tawayen Kurdawa masu neman ‘yantar da yankinsu.
www.rfi.fr
January 21, 2026 at 7:59 AM
Togo ta kori tsohon shugaban sojin Burkina Faso da ke zaman mafaka a ƙasar
Togo ta kori tsohon shugaban sojin Burkina Faso da ke zaman mafaka a ƙasar
Hukumomi a Togo sun kama tare da korar tsohon shugaban riƙon ƙwaryar Burkina Faso, wanda ke zaman mafaka, sakamakon zarginsa da ci gaba da shiryawa ƙasarsa zagon ƙasa, sai dai babu tabbas ko Burkina  Fason aka tura shi.
www.rfi.fr
January 20, 2026 at 2:29 PM
Sojojin Congo sun fara komawa birnin Uvira bayan janyewar M23
Sojojin Congo sun fara komawa birnin Uvira bayan janyewar M23
Sojojin Jamhuriyyar Congo da mayaƙan da ke taimaka musu a yaƙin da ƴan tawaye sun fara komawa sassan birnin Uvira na gabashin ƙasar kwanaki bayan janyewar mayaƙan M23 masu samun goyon bayan Rwanda.
www.rfi.fr
January 20, 2026 at 8:39 AM